News
Wata Tirela Ɗauke Da Kayan Buga Takardu Ta Faɗo Daga Saman Gada
Wata tirela mai ɗauke da kayan buga takardu ta faɗo daga saman gadar Oshodi a ranar Asabar, inda ta fadi cikin rami, lamarin da ya jawo raunin wani mutum.
A cewar Adebayo Taofiq, kakakin LASTMA, wanda abin ya rutsa da shi an ceto shi, aka kai shi asibiti domin kulawa. Direban tirelar kuma an kama shi, sannan aka mika shi ga ‘yan sanda a Makinde Police Station domin bincike.
Taofiq ya bayyana cewa birkin motar ne ya lalace yayin da take sauka daga Oshodi-Oke zuwa Mile 2, lamarin da ya sa direban ya rasa ikon sarrafa motar kafin ta faɗo ƙasa kamar yanda Jaridar platinum post news ta ruwaito
Advertisements
