Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Budewa Mota Dauke Da Fasinjoji  Wuta A Iyakar Kwara Da Kogi

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan wata mota dauke da fasinjoji a kan hanyar Ilorin–Egbe da ke tsakanin garuruwan Eruku da Egbe, a iyakar jihohin Kwara da Kogi, inda suka budewa mitar wuta.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da rana a ranar Asabar, lokacin da maharan suka fito daga daji suka fara harbin motar da ke dauke da fasinjoji.

Advertisement

K-MAN Ta Taya Rear Admiral Idi Abbas Murna Bisa Karin Matsayin Da Ya Samu 

Rahotanni sun bayyana cewa direban motar, wanda ɗan asalin Isanlu ne, ya samu raunuka sakamakon harbin bindigar ya ta same shi yayin harin.

Mazauna yankin sun roƙi shugabannin ƙananan hukumomin Yagba East da Yagba West da su haɗa kai wajen dakile irin waɗannan hare-hare da ke ƙara yawa a hanyar.

Advertisement

Hanyar Ilorin–Egbe, wacce ke da muhimmanci wajen sufuri da kasuwanci tsakanin jihohin Kwara da Kogi, ta zama cikin hanyoyin da ake yawan samun hare-haren ƴan bindiga a ‘yan watannin nan.

 

Advertisement

PLATINUM POST NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending