News
Zohran Mamdani Ya Zama Musulmi Na Farko Magajin Birnin New York, Birni Mafi Girma A Amurka
A Amurka, Musulmi na farko kuma dan jam’iyyar Democrats mai ra’ayin gurguzu Zohran Mamdani, ya lashe zaben magajin garin birnin New York a ranar Talata.
Nasarar ta matashin dan siyasar mai shekara 34 ta mayar da shi zuwa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan Siyasar Democrat a ƙasar ta Amurka.
DSP Barau Da Akpabio Kan Sambatun Trump : Jajirtaccen Shugabanci Da Tsoron Allah
Mamdani zai zama Musulmi na farko da zai zama magajin garin New York, babban birni a Amurka ne bayan ya doke tsohon Gwamnan jihar New York, Andrew Cuomo, mai shekaru 67.
Coumo wanda ya tsaya a matsayin dan takara mai zaman kansa bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani ya samu goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump.
Wannan zabe ya kasance wata alama ta fafatawa tsakanin masu ra’ayin tsohon salo da kuma sabo a jam’iyyar Democrat, kuma ana ganin sakamakon zai iya tasiri kan siyasar jam’iyyar a matakin ƙasa.
A jihar Virginia, jam’iyyar Democrat ta samu nasara inda Abigail Spanberger ta ci zaben gwamna, kuma ta zama mace ta farko da za ta rike wannan mukami a jihar
Baya ga nasarar Mamdani, masu kada kuri’a a fadin kasar Amurka sun goyi bayan ‘yan Democrats, da suka tsaya takarar neman kujerun gwamnoni a jihohin New Jersey da Virginia.
A New Jersey, Mikie Sherrill, ce ta lashe zaben gwamnan jihar inda Abigail Spanberger ta ci zaben gwamna a Virginia.
Masu zaben sun yi watsi da kiran Shugaba Donald Trumpna kada wa ‘yan takarar da yake so kuri’a inda suka zabi abinda ya kwanta musua rai.
‘Yan Democrats sun kuma samu nasara a jihar California, wacce ake sa ran za ta samu karin kujeru a majalisar wakilan Amurka.
Kodayake ‘yan takara da batutuwan cikin gida sun taka rawa, sannan ra’ayin masu zabe kan shugabancin Trump da manufofinsa shi ne ya fi tasiri, inda wannan zaben ya zama zakaran gwajin dafin tsarin mulkin shugaba Trump tun bayan dawowarsa kan mulki watanni tara da suka gabata.
A martaninsa, Trump ya wallafa sako a shafukan sada zumunta yana kare kansa bayan sakamakon ya fara fitowa, inda ya ce wasu masu fashin baki sun nuna cewa ba Trump ne ya shiga takarar da kansa ba.
