Connect with us

News

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ta Sace Kanta Don Ta Karbi Kudin Fansa Daga Hannun Mijinta

Published

on

1758622702522

Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama wata mata mai suna Chioma Ezebie Adaniken bisa zargin kitsa sace kanta tare da ɗan uwanta da wani abokin aikinta, da nufin karɓar kudin fansa daga Hannun mijinta.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikoedem, ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce matar ta haɗa baki da ɗan uwanta, Osita Godfrey, da wani matashi mai suna Martins Chidozie, domin shirya sacewarta da ɗanta mai shekara uku.

Advertisement

Zohran Mamdani Ya Zama Musulmi Na Farko Magajin Birnin New York, Birni Mafi Girma A Amurka

A cewar sanarwar, mijinta Paul Adaniken, ne ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na New Etete da ke Benin City, inda ya bayyana cewa matarsa da ɗansa sun ɓace bayan ya bar su a gida da safe. Daga baya, ya karɓi kira daga lambar da bai sani ba, inda aka ce an sace su, kuma masu garkuwar sun nemi naira miliyan biyar (₦5m) a matsayin kudin fansa.

ASP Ikoedem ta ce bayan samun rahoton, jami’an rundunar suka kaddamar da bincike mai zurfi da kuma amfani da dabarun leken asiri, wanda ya bayyana cewa ɗan uwanta Osita, wanda da farko ake ganin yana taimakawa ’yan sanda da bayanai, shi ma yana cikin lamarin.

Advertisement

“Binciken ya kai ga kama Osita Godfrey wanda ya amsa cewa shi ne ya taimaka wajen shirya satar, kafin daga bisani a kama matar da sauran abokan aikinta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce an kwato kuɗin fansar ₦5m da suka karɓa, yayin da ake ci gaba da bincike a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar.

Advertisement

 

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending