News
Dalilin Da Ya Sa Jihar Kano Ke Duba Yiwuwar Amfani Da Harshen Hausa Wajen Koyarwa A Makarantu
Majalisar dokokin Kano ta fara gwama muhawara kan wani ƙuduri da ke neman amfani da harshen Hausa wajen koyarwa a makarantu a faɗin jihar a hukumance kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Wannan ƙuduri an yi masa take da: “Ƙudurin Amfani da Harshen Uwa (Hausa) Wajen Koyarwa a Makarantu a Kano,” wanda ɗan majalisa Musa Kachako, mai wakiltar mazaɓar Takai daga jam’iyyar NNPP, ya gabatar.
An cafke ‘likitan bogi’, An Rufe Asibitin Da Yake Gudanarwa Ba Bisa Ƙa’ida Ba
A yayin da yake gabatar da ƙudurin, Kachako, ya ce wannan mataki zai ƙarfafa ilimi daga tushe da kuma dacewa da tsarin da duniya ke amfani da shi a duniya.
Ya kuma ce ƙasashe kamar Sin da Japan da India sun samu gagarumar cigaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harshen uwa wajen koyarwa a ilimi a matakin farko.
A cewarsa, koyarwa cikin Hausa, zai ƙara fahimtar karatu a tsakanin ɗalibai da rage faɗuwa jarrabawa da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da alkinta al’adun al’umma.
“Wannan ƙuduri zai taimaka wajen bai wa kowanne yaro damar samun ilimi a Kano,” in ji Kachako.
Bayan tattaunawar, shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Jibrin Ismail Falgore, ya miƙa ƙudurin ga kwamitin ilimi domin nazarin ƙudurin da ba da shawarwaru.
A ɗaya ɓangaren kuwa, Zakariyya Nuhu (NNPP–Gabasawa) ya gabatar da ƙudurin kafa kwalejin noma a mazaɓarsa.
Nuhu ya kuma ce wannan buƙata ta kafa kwalejin ilimin zai taimaka wajen inganta cigaban tattalin arziƙi kasancewar kaso 60% na mazauna garin manoma ne.
Haka kuma, majalisar ta karɓi wasiƙar neman buƙatar da samar da makarantar fasaha a ƙaramar hukumar Gaya da kafa hukumar kula da ƙananan hukumomi.
Kakakin majalisar dokokin ya miƙa wasiƙun biyu ga kwamitocin da suka dace domin duba su da ba da shawara.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
