Connect with us

News

An cafke ‘likitan bogi’, An Rufe Asibitin Da Yake Gudanarwa Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Published

on

IMG 20251109 WA0007 1536x866

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Enugu sun cafke wani mutum da ake zargin yin aikin likitanci ba bisa ƙa’ida ba, tare da rufe wani asibiti da yake gudanarwa a garin Obollo-Etiti, ƙaramar hukumar Udenu.

Mutumin mai suna Kenneth Mamah na gudanar da asibiti da ya sanya wa suna St. Joseph Memorial Hospital, ba tare da rajista, horo, ko izini daga hukumomin lafiya ba.

Advertisement

An Soke Tashin Jiragen Sama Fiye Da 2,000 A Amurka Yayin Da Harkokin Gwamnati Ke Ci Gaba Da Dagulewa

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a ta ma’aikatar, Ugodu Avemaria, ta fitar ranar Lahadi, an bayyana cewa samamen ya biyo bayan rahotanni daga jama’a da bayanan sirri da suka tabbatar da zargin. Samamen an gudanar da shi ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na Jihar Enugu, Dr. George Ugwu.

Binciken jami’ai ya nuna cewa, Ana gudanar da ayyukan tiyata a ɗakin da ake karɓar marasa lafiya, ba a ɗakin tiyata ba.

Advertisement

Wurin ba shi da tsafta, kuma babu kayan aiki da suka dace.

Babu ƙwararrun ma’aikata, kuma wanda ke gudanar da asibitin bai da lasisin likita.

Advertisement

Sanarwar ta ce: “Yana gudanar da ayyukan lafiya masu hatsari, ba tare da izini ko cancanta ba, yana jefa rayukan al’umma cikin haɗari.”

Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta yi kira ga jama’a da su rika kai rahoto kan duk wani wurin kiwon lafiya da ba ya bin ƙa’ida domin kare lafiya da rayuwar al’umma.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending