Connect with us

News

‎Sama Da ‘Yan Sanda Dubu 100 Ne Suke Gadin Manya Maimakon Ayyukan Tabbatar Da Tsaron Al’umma A Najeriya ‎ ‎—Rahoto

Published

on

‎Wani sabon rahoton ƙungiyar Tarayyar Turai ya bayyana cewa sama da jami’an ‘yan sandan Najeriya 100,000 ke aikin kare manyan ‘yan siyasa da fitattun mutane (VIPs), maimakon kare al’umma daga miyagun laifuka.

‎Rahoton, wanda Hukumar Tarayyar Turai kan lamuran mafaka (EU Agency for Asylum) ta wallafa a Nuwamba 2025, ya ƙiyasta cewa Najeriya na da jami’an ‘yan sanda 371,800, domin hidimar al’umma fiye da miliyan 236.

Advertisement

Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat

‎Sai dai, a cewar rahoton, an karkatar da kaso mai tsoka daga cikin waɗannan jami’ai zuwa gadin manya, abinda ke haifar da karancin jami’an sintiri da tsaron al’umma.

‎ “Ai akwai jami’ai 371,800, amma sama da 100,000 daga cikinsu suna aikin kare manya, maimakon ayyukan tabbatar da tsaron fararen hula,” in ji rahoton.

Advertisement

‎Rahoton ya ce sakamakon wannan matsala, Akwai jinkirin amsa kiran gaggawa idan laifi ya faru, Yankuna da dama ba su da jami’an tsaro, Laifuka na ƙaruwa ba tare da ɗaukar mataki da wuri ba.

‎Kazalika, EU ta nuna damuwa kan cin hanci, amfani da ƙarfi fiye da kima, kama mutane ba bisa ƙa’ida ba, da karancin kayan aiki a rundunar.

Advertisement

‎Rahoton ya tunatar cewa a Yuni 2023, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun ya ba da umarnin janye jami’an rundunar MOPOL daga aikin gadin VIPs, domin tura su ayyukan tsaron kasa.

‎An sake maimaita wannan umarni a Afrilu 2025, amma duk da haka “Har yanzu yawancin jami’an na cigaba da gadin manya.”

Advertisement

‎Masana na ganin cewa muddin ba a sauya amfani da jami’an tsaro daga kare masu mulki zuwa kare talakawa ba, matsalar tsaro a Najeriya za ta cigaba da dagulewa, musamman a yankunan karkara.

 

Advertisement

BUSINESS DAILY 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending