News
Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa ‘Yan Najeriya Huɗu Hukuncin Ɗaurin Shekaru 55 Kan Satar Wayoyi
Kotun Kingston Crown Court da ke birnin London ta yanke wa wasu mutane hukuncin ɗaurin shekaru 55 a gidan yari, bayan da aka same su da laifin shiga wata kungiyar masu fashin shagunan wayoyi da sauran na’urorin zamani.
A cewar rahoton ‘yan sanda, kungiyar ta kai hare-hare daban-daban har 13 tsakanin Satumba zuwa Nuwamba 2024, inda suke amfani da barazana, karfin tuwo da tashin hankali domin tsoratar da ma’aikata, tare da tilasta su bude rumbunan ajiya kafin su kwashe kayayyaki masu daraja.
An kiyasta darajar kadarorin da suka sace a lokacin kai hare-haren da fam 240,000, wanda ya hada da wayoyi masu tsada da sauran kayan lantarki na zamani.
‘Yan sanda sun ce nasarar cafke su ya biyo bayan shaidun DNA, bayanan kiran waya, da kuma na’urorin bin sawun motocin da suka yi amfani da su wajen gudanar da laifukan.
Bayan kama su, jami’an tsaron sun kai samame gidajen da aka alakanta da su, inda aka kwato wasu daga cikin wayoyin da aka sata, tare da wasu muhimman hujjojin bincike da suka kara tabbatar da laifinsu.
A jimlace, mutane 10 ne aka gurfanar a gaban kotu, inda akasari suka amsa laifin hada baki da aikata fashi.
An yanke wa mafi yawansu hukuncin shekaru 2 zuwa 10 a gidan yari, yayin da wasu biyu suka samu sassaucin hukunci, saboda amincewa da laifi tun farkon shari’ar, tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.
Jami’an ‘yan sanda sun jaddada cewa wannan hukunci ya nuna irin tsauraran matakan da hukumomin Birtaniya ke dauka kan masu aikata manyan laifuka, musamman masu karya doka
