Connect with us

News

Wani Ɓarawo Ya Kutsa Fadar Gwamnatin Kano Ya Sace Mota

Published

on

Wani ɓarawo ya kutsa fadar gwamnatin Kano da sassafiyar Litinin ɗinnan, inda ya tsere da ɗaya daga cikin motar Hilux ɗin ayarin mataimakin gwamna.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ɓarawon ya shiga ta Gate na huɗu sannan ya fice ta babban ƙofar fadar bayan ya kunna motar da ya sace da misalin ƙarfe 5 na safe.

Advertisement

Jami’an Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

An gano satar ne bayan da Na’urar CCTV ta nuna yadda lamarin ya faru. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro ba sa yawan sintiri a ofishin mataimakin gwamna sai idan yana nan ko lokacin aiki.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an kama direban motar, Shafiu Sharp-Sharp, domin bincike, yayin da CSO ke nazarin bidiyon tsaron.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending