Connect with us

News

‎Tirela Ta Murkushe Yaran Mota Har Lahira 

Published

on

Danfo conductor main 1 e1487247821282

Wani Yaran mota ya rasa ransa a daren Laraba a yankin Ogolonto da ke Ikorodu, bayan da wata babbar motar ɗaukar kaya ta murkushe shi yayin da take motsi.

‎Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 11 na dare, kuma hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da binciken yadda ya faru.

Advertisement

TALLAFIN GWAMNATI: Kashi 44 cikin 100 Ne Kaɗai Ke Isa Ga Masu Buƙata A Najeriya —Rahoto

‎Shaidu a wurin sun ce matashin ya faɗa a ƙarƙashin motar ne yayin da yake ƙoƙarin daidaita motar ɗauke da kaya, inda tayoyin motar suka bi ta jikinsa, suka kashe shi a nan take.

‎Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Lagos (LASTMA), Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce jami’an rundunar “Special Night Patrol Team” ta LASTMA sun kama direban motar.

Advertisement

‎A cewar Bakare-Oki, binciken farko ya nuna cewa marigayin ya sauko daga motar domin sanya katako a ƙarƙashin tayoyi saboda matsalar birki. Sai dai a yayin wannan yunƙuri ne ya zame ya faɗa, motar kuma ta murkushe shi.

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending