News
Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Janar Christopher Musa A Matsayin Sabon Ministan Tsaro
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya.
Shugaban kasar ya sanar da wannan naɗin ne cikin wasiƙar da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talata, bayan murabus ɗin tsohon ministan, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, a ranar Litinin.
