Connect with us

News

‎Idan Dokokin Yaki Da Rashawa Suka Yi Aiki Yadda Ya Kamata, Kashi 80% Na ’Yan Najeriya Za Su Iya Fuskantar Hukunci ‎ ‎ – ICPC

Published

on

ICPC ta maka tsohon hadimin El Rufa’i kotu bisa zargin almundahana

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Kare Hakkokin Jama’a ICPC ta bayyana cewa matsalar rashawa a Najeriya ta yi zurfi matuka, inda ta ce idan aka aiwatar da dokoki yadda ya kamata, kusan kashi 80% na ‘yan kasa na iya fuskantar hukunci.

‎Bayanin hakan ya fito ne daga Kwamishinan hukumar ICPC na Kaduna, Sakaba Ishaku, a taron horaswa kan inganta gaskiya da rikon amana a kananan hukumomi.

Shugaba Tinubu Ya Kara Jaddda Umarnin Janye ’Yansanda Daga Gadin Manyan Mutane

‎A yayin jawabin nasa, Ishaku ya yi nuni da cewa matsalar rashawa a Najeriya ta zama ruwan dare, inda ya ce ta yi katutu a kusan dukkan matakan gwamnati da zamantakewar al’umma.

‎Ya ce: “Idan aka aiwatar da doka yadda ya kamata, kimanin kashi 80 cikin 100 da kuke gani suna yawo a titi za su kasance cikin gidan yari.”

‎Kwamishinan ya bayyana yadda rashawa ta janyo wa Najeriya koma-baya ta fannoni da dama—daga karkatar da kudaden gwamnati, zuwa ƙara talauci da haifar da rashin tsaro, tare da gurgunta ci gaban kasa.

‎Ishaku ya ce “ba a samun tarin manyan dukiyoyi ba tare da wani nau’i na kaucewa doka ba”, yana mai cewa mafi yawan arzikin da ake gani akwai abin da bai yi daidai ba a tushensa, ko dai ta hanyar takura ma’aikata ko kuma wani nau’i na almundahana.

Advertisement

‎Ya kuma koka kan yadda wasu ’yan Najeriya ke kin goyon bayan yaki da rashawa saboda amfanin da suke ɗibawa daga tsarin da ba na gaskiya ba. “Ba kowa yake son a ji ana yaki da rashawa ba, saboda wani lokaci tana karya yarjejeniyar amfanarda-juna tsakanin wasu,” in ji shi.

‎Sai dai Ishaku ya yi suka ga shugabannin kananan hukumomi da ke kammala wa’adinsu ba tare da wani abin a-zo-a-gani ba. Ya ce hakan na rage darajar shugabanci, yana tambayar ko irinsu ma sun cancanci riƙe mukaman da ake basu.

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending