Connect with us

News

Ba Za Mu Taba Yafe Wa Wadanda Suka Yi Wa ‘Yan Uwanmu Kisan Gilla Ba — Sheikh El-Zakzaky

Published

on

Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky

Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya ce zai yi hisabi da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban Allah kan abin da ya faru a Zariya a 2015.

Rikicin ya fara ne bayan da mambobin IMN sun tare wa tsohon Hafsan Soji, Tukur Buratai, hanya.

Advertisement

‎Idan Dokokin Yaki Da Rashawa Suka Yi Aiki Yadda Ya Kamata, Kashi 80% Na ’Yan Najeriya Za Su Iya Fuskantar Hukunci ‎ ‎ – ICPC

Lamarin fara a matsayin ƙaramin rikici daga baya ya rikiɗe zuwa babban al’amari, lamarin da ya sanya sojoji buɗe wa mabiyan wuta.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da kwamitin bincike na jihar, sun bayyana cewa an kashe tare binne ɗaruruwan mambobin IMN a asirce bayan faruwar lamarin.

Advertisement

Daga baya an kama Zakzaky da matarsa, an tsare su har zuwa 2021, kafin daga baya kotu ta wanke su.

Bayan cikar lamarin da shekara 10, Zakzaky ya ce gwamnati ta kasa ɗaukar alhakin abin da ya faru.

Advertisement

Ya ce: “Babu abin da aka yi. Ba su yadda cewa wani abu ya faru ba, duk da cewa kwamitin bincike ya miƙa rahotonsa tun 2016.”

Zakzaky, ya kuma zargi gwamnatin yanzu da yin shiru a kan lamarin, duk da alƙawarin da ta yi na duba rahoton da kuma biya iyalan waɗanda abin ya shafa diyya.

Advertisement

Ya ce: “Sun tabbatar mana cewa za su magance batun, amma tun daga lokacin shiru kake ji.”

Da aka tambaye shi ko ya yafe wa Buhari, Zakzaky, ya ce ya bar komai a hannun Allah, kuma zai masa hisabi da shi ranar gobe ƙiyama.

Advertisement

Zakzaky ya ce: “Game da Buhari, za mu gana a Ranar Alƙiyama. Lissafin Buhari ya ƙare.”

Ya ƙara da cewa harin bai yi nasarar daƙile IMN ba, sai ma ƙara ɗaukaka sunan ƙungiyar inda ta yi fice a duniya.

Advertisement

Zakzaky, ya ce sun kai ƙarar lamarin kotun ƙasa da ƙasa, sannan ƙofarsu a buɗe ta ke domin tattaunawa da gwamnati.

Ya ce: “Ko ba sa son ganinmu, za su gan mu. Ko ba sa son jinmu, za su ji mu.”

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending