Connect with us

News

Kotun Koli Ta Soke Afuwar Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Maryam Sanda

Published

on

FB IMG 1765537168853

Kotun Ƙolin Nijeriya ta soke afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, wacce aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarar 2020 saboda kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

A hukuncin da ta yanke a ranar Jumma’a a babban birnin ƙasar Abuja, Kotun Kolin ta sake tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda.

Kotun Koli Ta Soke Afuwar Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Maryam Sanda

A watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya yi was Maryam afuwa ta hanyar sassauta mata hukuncin daga na kisa zuwa na zaman gida yari na shekaru 12 a bisa dalilai na tausayawa.

Alkali Moore Adumein wanda ya jagoranci yanke hukuncin ya ce

ba daidai ba ne Shugaban Kasa ya nemi yin amfani da ikon yin afuwa a kan wata shari’ar kisan kai da aka aikata, wadda ake jiran hukuncin ƙarar da aka ɗaukaka a kanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending