News
Jami’an NAFDAC Sun Yi Gargadi A Daina Cin Indomie Mai Ɗanɗanon Kayan Lanbu
Jami’an Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) sun ayyana taliyar Indomie mai dandanon ganyayyaki (Vegetable Flavour) a matsayin abinci mai hadadri ga lafiyar mutane, ta umarci a bi kasuwanni a kwashe su kaff don kiyaye lafiyar mutane,
A cikin Sanarwa mai Lamba 041/2025 da aka wallafa a ranar Juma’a, NAFDAC ta ce hukumar kare lafiyar masu saye ta Faransa, Rappel Conso, ta bayar da umarnin janye Indomie mai ɗanɗanon kayan lambu bayan gwaje-gwaje sun tabbatar da kasancewar sinadaran da ba a bayyana ba, musamman madara da ƙwai, a cikin samfurin.
Jami’an NAFDAC Sun Yi Gargadi A Daina Cin Indomie Mai Ɗanɗanon Kayan Lanbu
Waɗannan sinadaran ba a ambace su a jikin lakabin samfurin ba, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiyar mutanen da ke da samun matsala da wasu abinci (allergy) ko matsalar jure wasu sinadarai, inda hakan ka iya jawo mummunan lahani ga lafiyarsu.
Janyewar ta shafi dukkan rukunan samfurin da ke da ranar ƙarewa ta 6 ga Fabrairu, 2026, duk da cewa sanarwar ba ta fayyace ƙasar da aka ƙera samfurin ba.
NAFDAC ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne a matsayin kariyar lafiyar jama’a, domin rage haɗarin da samfurin ke haifarwa ga masu fama da matsalar rashin jituwa da wasu abinci.
Hukumar ta ƙara da cewa ko da yake yiwuwar shigowar wannan samfurin cikin Najeriya tana da tsauri, sakamakon haramcin shigo da taliya (noodles) da gwamnatin tarayya ta yi, amma ba za a iya kawar da yiwuwar shigowarsa ta hanyoyi haramtattu ba, kamar saye ta yanar gizo ko shigowar mutum daga ƙasashen waje.
Domin hana yaduwar Indomie mai ɗanɗanon kayan lambu a cikin ƙasar, NAFDAC ta umurci dukkan daraktocin shiyya-shiyya da masu kula da jihohi da su ƙara sa ido tare da gaggauta kwace wa da kwashe duk wani samfurin da aka samu a kasuwanni, rumbunan ajiya, ko sarkar rarrabawa.
Bugu da ƙari, NAFDAC ta bukaci jama’a da su rika bayar da rahoton duk wata illa ko matsalar lafiya da aka samu bayan cin samfurin ta hanyoyin rahoto na intanet na hukumar.
PREMIUM TIMES
