Connect with us

News

Hukumar NAFDAC tace ta kasance cikin shirin ko ta kwana biyo bayan gano sinadarin Ethylene Oxide a cikin Indomie

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta kasance cikin shirin ko ta kwana biyo bayan gano sinadarin Ethylene Oxide a cikin Indomie instant Noodles ‘Special Chicken flavor’ mai iya haddasa cutar daji.

 

Advertisement

Mai magana da yawun hukumar a Kano a ranar Talata, Nura Muhammad Rabiu yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin da jaridar Blazon News Nigeria ya ce, tuni aka tura jami’an hukumar da za su janye samfurin domin tantance lab da kuma matakin da za a dauka don kare lafiyar jama’a.

MATSALAR KWACEN WAYA A KANO YA ZAMA  BABBAR BARAZANA GA LAFIYA DA KUMA ZAMANTAKEWAR AL, UMMAR JAHAR KANO. 

 

Advertisement

A cewarsa, ma’aikatun lafiya na kasashen Taiwan da Malaysia ne suka gano hakan wanda ya tabbatar da cewa sinadarin da aka samu a cikin samfurin yana da alaka da kamuwa da cutar daji.

 

Advertisement

Haka kuma yace a matsayin su na masu kula da al’amuran yau da kullun, zasu ɗauki matakan gaggawa don ganin samfurin bai bazu ba a fadin kasar nan , har ma da sauran nau’ikan noodles ɗin nan take a kasuwannin Najeriya

 

Advertisement

 

Yakara da cewa suna tabbatar wa jama’a cewa za a yi cikakken bincike kuma za a sanar da sakamakon binciken nasu .  A halin yanzu, suna kira ga jama’a da su yi taka tsantsan game da samfurin har sai sakamakon binciken da suka gudanar ya fito

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending