Connect with us

News

Jami’an NAFDAC Sun lalata Jabun Magunguna Da Kayayyaki Na Sama Da Naira Biliyan 64 A Kano Da Oyo

Published

on

Wasu kayayyaki da NAFDAC ta lalata

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta lalata magunguna da kayan abinci marasa inganci da kuma waɗanda wa’adinsu ya ƙare, wadda darajarsu ta kai Naira biliyan 65 a jihohin Kano da Oyo.

A Jihar Kano, NAFDAC ta lalata sama da tan 618 na magunguna da sauran kayayyakin da aka haramta ko wa’adinsu ya ƙare, waɗanda darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 10.1.

Advertisement

Mutum 195 Sun Mutu A Dalilin Kamuwa Da Cutar Zazzabin Lassa A Najeriya  —NCDC

An gudanar da aikin lalata kayayyakin ne a yankin Kalibawa, da ke kan hanyar Kano zuwa Daura.

An ƙwato kayayyakin daga jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai: Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sakkwato da Zamfara.

Advertisement

A Jihar Oyo kuma, hukumar ta lalata magunguna, kayan shafe-shafe da na abinci marasa inganci, waɗanda wa’adinsu ya ƙare ko kuma aka haramta amfani da su, kuma darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 55.

An gudanar da aikin a wajen zubar da shara ta yankin Moniya da ke kan titin Akinyele a Ibadan.

Advertisement

Wannan aiki ya nuna yadda hukumar ke aiki don kawar da kayayyakin da ba su da inganci daga kasuwanni.

Daraktar Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce wannan aiki saƙo ne ƙarara ga masu safarar kayan bogi cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen ayyukansu da ke jefa rayukan ’yan Najeriya cikin hatsari.

Advertisement

Ta ce NAFDAC na da alhakin kare lafiyar jama’a tare da tabbatar da cewa dukkanin kayan abinci, magunguna, kayan shafe-shafe, na’urorin kiwon lafiya da sinadarai da ake amfani da su a Najeriya sun cika ƙa’idoji.

Ta ƙara da cewa lalata kayayyakin na daga cikin dabarun da hukumar ke amfani da su domin hana kayayyakin komawa kasuwa.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending