News
Mutum 195 Sun Mutu A Dalilin Kamuwa Da Cutar Zazzabin Lassa A Najeriya —NCDC
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa Najeriya ta fi samun yawan mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da zazzabin lassa a shekarar 2025 da 2024 domin a 2025 cutar ta yi ajalin mutum 195 a kasar nan.
Hukumar ta ce duk da haka ana samun nasarar dakile yaduwar cutar a Najeriya.
Shugaba Tinubu Ya Gabatar Kasafin Kuɗin Shekarar 2026 Wanda Ya Kai Naira Triliyan 58.47
NCDC ta bayyana wadannan alkalumar a matsayin sakamakon yaduwar cutar na mako 49 a shafinta dake yanar gizo.
Rahotan yaduwar cutar ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutum 195 daga cikin mutum 1,069 din da aka tabbatar sun kamu da cutar a 2025.
Sakamakon ya nuna cewa an samu karin mutum kashi 1.7% idan aka kwatanta mutum kashi 18.5% din da aka samu a 2025 da kashi 16.5% din da aka samu a 2024.
An Samu Karuwa a Yawan Mutanen dake Kamuwa da Zazzabin Lassa a Mako na 49.
Hukumar ta tabbatar cewa an samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar daga mutum 24 a mako na 48 zuwa mutum 33 a mako na 49.
NCDC ta ce an samu karuwan ne a jihohin Bauchi, Ondo, Edo da Taraba.
Hukumar ta Kuma ce a cikin mako na 49 an samu mutum 143 da ake zargin sun kamu da cutar inda daga cikin su mutum 8 sun mutu a kananan hukumomi 10 dake jihohi hudu a kasar nan.
A takace dai a shekarar 2025 luma a mako na 49 mutum 9,041 ne ake zargin sun kamu da cutar inda daga cikin su aka tabbatar da mutum 1,069 da suka kamu da cutar da mutum 195 da cutar ta yi ajalinsu sannan da wasu mutum biyu da ba a tabbatar da matsayinsu game da kamuwa da cutar ba a kananan hukumomi 103 dake jihohi 21.
Sannan a mako 49 na shekarar 2024 mutum 9.492 ne ake zargin sun kamu da cutar inda daga cikin su aka tabbatar da mutum 1,154 sun kamu da cutar mutum 10 ba a tabbatar da matsayin su game da kamuwa da cutar ba a kananan hukumomi 137 da jihohi 28.
A kwatance dai hakan na nuna cewa cutar ya fi yaduwa a shekarar 2024 fiye da shekarar 2025.
Hukumar ta tabbatar cewa duk da cewa an samu raguwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar amma har yanzu an ci gaba da samun karuwa a yawan mutanen dake mutuwa a dalilin cutar a 2025.
Matasa Sun Fi Yawa a Rukunin Mutanen dake Kamuwa da Cutar.
Hukumar ta shafa cewa matasa musamman masu shekaru 21 zuwa 30 sun fi yawa a rukunin mutanen da suka fi kamuwa da cutar sannan mutane masu shekaru 30 zuwa 96 na daga cikin masu kamuwa da cutar.
NCDC ta kuma rawaito cewa mata sun fi maza yawan kamuwa da cutar a kasar nan.
A cikin mako na 49 na yaduwar cutar babu jami’in lafiyar da ya kamu da cutar.
