Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Gabatar Kasafin Kuɗin Shekarar 2026 Wanda Ya Kai Naira Triliyan 58.47

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya nemi a kara yawan kasafin kudin 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa da majalisun dokokin ƙasa kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai Naira triliyan 58.47.

A cewar shugaban ƙasar, an ware Naira triliyan 26.08 don ayyukan raya ƙasa, yayin da ayyukan yau da kullum zasu laƙume Naira triliyan 15.25.

‎Gwamna Yusuf Ya Karɓi bakuncin Shugabar Jami’ar Northwest Farfesa Amina Bayero. Mace Ta Farko a Jami’ar

Kasafin ya dogara da farashin gangar mai dala akan Dala 64.85.

Jimillar kuɗaɗen shigar da ake sa ran samu a 2026 sun kai Naira triliyan 34.33.

Kasafin ya kuma dogara da samar da gangar mai miliyan 1.84 a rana, da kuma farashin musayar kuɗi ₦1,400/$1.

Fannin tsaro zai laƙume Naira triliyan 5.41.

Advertisement

Manyan Ayyukan Gine-gine: Naira 3.56 tiriliyan

Ilimi: Naira triliyan 3.52 tiriliyan

Lafiya: Naira triliyan 2.48 tiriliyan

Tinubu ya bayyana kasafin da taken “Kasafin Haɗin Kai, Sabuwar Juriya da Rabon Arziki ga Kowa”, yana mai cewa kasafin ba wai takardun lissafi bane kaɗai, “bayyana fifikon ƙasa ne,” tare da alƙawarin dorewar kuɗi, gaskiya a bashi, da kashe kuɗi bisa ƙima.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending