News
Jami’an NAFDAC Sun Kona Jabun Kayayyaki Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa
DAGA ZUBAIRU LAWAL
Jami’an Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) sun lalata kayayyaki marasa inganci da jabun magunguna da kudinsu ya kai kusan Naira biliyan 5 a birnin Lafiya, Jihar Nasarawa.
An gudanar da kona kayayyakin ne a shingen zubar da shara na Angwan Rere, inda aka tattara su daga jihohin Nasarawa, Benue, Kogi, Neja da Filato da ke Arewa ta Tsakiya.
KANO: Ba A Samu Asarar Rai Ba A Gobarar Da Ta Tashi A Babban Asibitin Rogo
Da take jawabi, Daraktar-Janar na Hukumar NAFDAC, Farfesa Christianah Adeyeye, wadda Daraktan Yankin Arewa Ta Tsakiya, Mista Kenneth Azikiwe, ya wakilta, ta ce kayayyakin an gano su ne sakamakon sintirin da jami’an hukumar ke gudanarwa domin dakile yaduwar kayayyaki masu barazana ga lafiya.
Ta ce kayayyakin da aka lalata sun haɗa da ,abincin masana’antu marasa inganci,, kayan ƙara dandano,, magunguna ƙirƙira, na’urorin lafiya na bogi, kayan kwalliya marasa inganci, sabulai da sinadarai na ƙarya.
Farfesa Adeyeye ta bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin an ɓoye su da gangan, wasu kuma ‘yan kasuwa masu gaskiya ne suka miƙa su ga hukumar bayan sun gano hadarinsu, domin kare lafiyar al’umma.
Ta jaddada cewa NAFDAC za ta ci gaba da tabbatar da cewa ingantattun kayayyaki kaɗai ake sayarwa a kasuwanni, tare da kira ga jama’a su rika ba da bayanai kan duk inda ake jabun kayayyaki.
A nasa bangaren, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Nasarawa, Usman Baba, wanda ya wakilci gwamnatin jihar, ya yaba wa NAFDAC kan wannan aiki na tsarkake kasuwanni, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga hukumar.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
