Connect with us

News

KANO: Ba A Samu Asarar Rai Ba A Gobarar Da Ta Tashi A Babban Asibitin Rogo

Published

on

Shugaban  Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, ya ce babu wanda ya rasa ransa a gobarar da ta tashi a wani bangare na Babban Asibitin Rogo da ke jihar Kano.

Advertisements
Advertisements

A cewar sa, gobarar ta haifar da ɗan razana ga marasa lafiya da ma’aikatan jinya, kafin jami’an kashe gobara da mazauna yankin su shawo kan ta.

Advertisements

Jami’in Yaɗa Labarai na Karamar Hukumar, Abdu Bako Abdullahi (ANIPR), ya ruwaito cewa lamarin ya haddasa asarar dukiyoyi masu daraja, inda ya yi kira ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba halin da al’umma suka shiga.

Advertisements
Advertisements

Ya ce sake fasalin asibitin zai taimaka wajen farfaɗo da hidimar kiwon lafiya a yankin, musamman ma matakin farko.

Alhaji Abubakar ya kuma yaba wa jami’an tsaro da Hukumar Kashe Gobara kan yadda suka tashi tsaye wajen dakile wutar cikin gaggawa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending