News
Jami’an Hukumar NAFDAC Sun lalata Tramadol Guda 491,000 A Kano
Jami’an Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, wato NAFDAC, sun lalata Tramadol guda 491,000 da aka kama a Jihar Kano, a wani yunkuri na kare lafiyar jama’a daga barazanar haramtattun magunguna.
Tramadol ɗin na nau’in 225mg an kama su ne a ranar 28 ga watan Mayu, 2025, lokacin da jami’an Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa suka cafke su a yankin Mai Gatari da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Jihar Nasarawa Ba Mafaka Bace Ga Masu Laifi — Inji Gwamna Sule
An bayyana cewa waɗanda suka shigo da magungunan sun gudu bayan jami’an kwastam sun dakile yunkurin su.
Babban daraktan bincike da aiwatar da dokoki na NAFDAC, Dr. Martins Iluyomade, ne ya jagoranci kona kwayoyin a madadin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye.
Farfesa Adeyeye ta ce, “Adadin Tramadol da aka kama ya kai 491 jarka, wato kimanin 491,000 a dunkule. An ƙiyasta darajar su a kasuwa da naira miliyan 91.”
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
