News
Jihar Nasarawa Ba Mafaka Bace Ga Masu Laifi — Inji Gwamna Sule
DAGA ZUBAIRU LAWAL
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta karyata zargin da ake yadawa cewa tana bai wa masu aikata kisan gillar da ya auku a Jihar Benue mafaka a cikin jihar.
Mai taimakawa Gwamna Abdullahi Sule kan harkokin yaɗa labarai, Alhaji Ibrahim Addra, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) da ke Lafia ranar Laraba.
Alhaji Addra ya mayar da martani ne kan wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda wani fitaccen ɗan siyasa daga Benue, Farfesa Zacharys Anger Gundu, ya zargi Gwamna Abdullahi Sule da cewa wai yana ɓoye wasu makiyaya da ake zargi da kai hari kan ‘yan kabilar Tiv.
A cewar Addra, “Zarge-zargen da Farfesa Gundu ke yadawa ba su da tushe, kuma suna da nufin tunzura jama’a da tayar da ƙayar baya tsakanin jihohin Benue da Nasarawa.”
Ya ce Gwamna Sule da gwamnatin sa ba za su taɓa mara wa masu laifi baya ba, kuma suna goyon bayan hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.
“Idan Farfesa Gundu yana da hujjoji a kan waɗannan zarge-zarge, ya gabatar da su ga hukumomin tsaro. Amma in babu, to ya fito fili ya janye kalamansa tare da neman afuwa,” in ji Addra.
Gwamnatin Nasarawa ta ce duk da cewa tana jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe a harin da ya faru a Benue, hakan ba ya nufin za a ɗora mata nauyin laifin da ba ta da hannu a ciki.
Addra ya ƙara da cewa gwamnatin Nasarawa za ta ɗauki matakin shari’a idan har irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe suka ci gaba da yaduwa.
“Zamana lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar jihohin Benue da Nasarawa na da muhimmanci, kuma gwamnati ba za ta yarda wani ya tayar da hankali ko tayar da fitina ba,” in ji shi.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
