News
Rundunar Sojojin Sama Ta Halaka ’Yan Ta’adda 95 A Neja
Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta halaka akalla ‘yan bindiga 95 a wani hari da ta kai ta sama a kauyukan Ragada da Warari da ke ƙaramar hukumar Rijau a Jihar Neja.
Wata majiya daga hukumar leken asiri ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa jiragen yaki na NAF sun gano ‘yan bindigar ne da misalin ƙarfe 3 na rana, a ranar Talata, yayin da suke ƙetare daga Jihar Zamfara ta hanyar Kebbi zuwa yankin Neja.
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Fara Hutun Makarantun Firamare Da Sakandare
An ce ‘yan bindigar na tafe da babura 108, dauke da muggan makamai, inda suka nufi kauyukan Warari da Ragada da ke cikin ƙaramar hukumar Rijau.
Haka zalika daga cikin ‘yan bindigar, 13 ne kawai suka tsere, yayin da sauran suka mutu a harin jiragen saman.
Majiyoyin tsaro sun ce harin na daga cikin matakan da ake ɗauka a karkashin Operation Fagge Fasan Yamma, domin dakile ta’addanci da ayyukan ‘yan fashi da makami.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
