Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Fara Hutun Makarantun Firamare Da Sakandare

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa daga ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025 ne za a fara hutun zangon karatu na uku a dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke koyar da karatun firamare da sakandare a fadin jihar, ciki har da makarantun kwana.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar a ranar Talata, inda ya bukaci iyaye da masu kula da ɗaliban makarantun kwana da su shirya tsaf domin karɓar ‘ya’yansu tun daga safiyar ranar hutun.

Advertisement

Ƙudirin Dokar Hana Jami’an Gwamnati Amfani Da Asibitoci Da Makarantun Kuɗi Ya Tsallake Karatun Farko

Sanarwar ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, yayin da ɗaliban makarantun rana za su koma a washegari, Litinin, 8 ga Satumba, 2025.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ya ja hankalin iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da bin wannan jadawalin kamar yadda aka tsara, yana mai cewa duk ɗalibin da ya ƙi dawowa makaranta a kan lokaci zai fuskanci hukunci.

Advertisement

Dr. Makoda ya kuma nuna godiyarsa ga iyaye da al’ummar Kano bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa ma’aikatar ilimi, yana mai kira da a ci gaba da haka domin ci gaban ilimi a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending