News
Ƙudirin Dokar Hana Jami’an Gwamnati Amfani Da Asibitoci Da Makarantun Kuɗi Ya Tsallake Karatun Farko
Majalisar Wakilai ta fara duba wani kudiri da ke neman hana jami’an gwamnati da iyalansu amfani da asibitocin kuɗi da makarantun masu zaman kansu a Najeriya.
Ɗan majalisar da ya gabatar da kudirin, Hon. Amobi Ogah, mai wakiltar mazaɓar Isuikwuato/Umunneochi daga Jihar Abia, ya ce an tsara dokar ne domin tilasta wa jami’an gwamnati amfani da cibiyoyin gwamnati.
Ƙauyuka 739 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa A Najeriya —NIHSA
A yayin da ya ke bayyana manufar kudirin, Hon. Ogah ya ce makasudin hakan shi ne farfaɗo da asibitoci da makarantun gwamnati da kuma rage yawan kuɗin da ake ɓarna da su wajen neman magani ko ilimi a waje.
“Yanzu haka cibiyoyinmu na lafiya da ilimi suna fama da matsaloli da dama saboda shugabanni ba sa amfani da su. Maimakon haka, suna tura ’ya’yansu zuwa makarantun masu tsada a cikin gida da ƙasashen waje, sannan su kan je ƙasashen waje domin neman magani,” in ji shi.
Ya ce idan har an tilasta wa shugabanni amfani da makarantun da asibitocin gwamnati, hakan zai sa su fara kulawa da su domin suna da muradin amfana da ingancinsu kamar sauran ’yan ƙasa.
Majalisar dai ta karanta kudirin a matakin farko a zaman da aka gudanar ranar Talata, kuma ana sa ran ci gaba da nazari a matakai na gaba kafin a yanke hukunci a kansa.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
