Connect with us

News

Ƙauyuka 739 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa A Najeriya ‎ —NIHSA ‎ ‎

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) ta sake fitar da wani gargaɗi mai ga al’ummar Najeriya, inda ta bayyana cewa jihohi 28 da Babban Birnin Tarayya (FCT), ciki har da Jihar Jigawa, na fuskantar barazanar ambaliya daga ranar 22 ga Yuli zuwa 5 ga Agusta, 2025.

‎Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Injiniya Umar Mohammad, ya fitar, yana mai cewa hasashen ya samo asali ne daga rahoton nazarin ambaliya na shekara-shekara da hukumar ta fitar tun a watan Afrilun bana.

Advertisement

Farfesa Adamu Gwarzo Ya Samu Lambar Girmamawa Daga Jaridar Blueprint Kan  Bunkasa Ilimin Jami’a A Najeriya 

‎A cewar sanarwar, akwai alamar ambaliya mai tsanani da za ta iya shafar ƙananan hukumomi 162 da ƙauyuka 739 a sassa daban-daban na ƙasar nan, sakamakon yawan zubar ruwan sama da kuma cikr dam-dam da koguna.

‎Daga cikin jihohin da aka lissafo a matsayin masu hadarin ambaliya akwai: Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Babban Birnin Tarayya (FCT), Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ondo, Filato, Rivers, Sokoto, Taraba da Yobe.

Advertisement

‎NIHSA ta bayyana cewa, birane da cibiyoyin kasuwanci da tattalin arziki kamar Abuja da Legas ma ba su tsira daga hatsarin ambaliya ba, inda take nuna fargabar cewa za a samu tsaiko a harkokin rayuwa da na tattalin arziki, idan ambaliyar ta auku.

‎Sanarwar ta kuma fayyace cewa ambaliya za ta iya katse hanyoyin mota sama da 100 da ke haɗa jihohi da dama, ciki har da: Okene-Lokoja-Abuja, Birnin Kebbi-Bunza da Ibi-Wukari. Hakazalika, wasu manyan tituna da ke Legas, FCT da yankin Neja Delta na cikin hadarin rufta.

Advertisement

‎Haka kuma, rahoton ya ce gidaje da shaguna da ababen more rayuwa da ke cikin yankunan da ke fuskantar ambaliya na iya fuskantar rushewa, lamarin da zai iya jefa dubban mutane cikin halin ƙa-ka-ni-ka-yi da tabarbarewar rayuwa.

‎Baya ga haka, filayen noma da gonaki da dama na cikin hatsarin bacewa, wanda hakan ke nuna alamun barazana ga wadatar abinci a wasu yankunan ƙasar nan.

Advertisement

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending