News
Ghana Ta Sanar Da Rage Harajin VAT A Farkon Sabuwar Shekara
Gwamnatin Ghana ta kudiri aniyar gabatar da sabbin sauye-sauye a bangaren haraji, inda ta ce za ta zaftare wani kaso daga cikin harajin kayayyaki na VAT daga 1 ga Janairu, 2026, ciki har da rage kaso na harajin domin sauƙaƙa wa al’umma da ’yan kasuwa yawan kuɗi.
Hukumar tara haraji ta ƙasar, Ghana Revenue Authority (GRA), ta ce sabon tsarin zai rage harajin VAT zuwa kashi 20 cikin 100, tare da ɗaga adadin kuɗin da kasuwanci zai kai kafin a tilasta masa bayan VAT.
Yadda Wani Matashi Ya Yi Ajalin Ɗan’uwansa Kan Bashin Naira 4,000
A cewar GRA, an ƙara ƙa’idar bayan VAT daga cedi 200,000 zuwa cedi 750,000, matakin da ake sa ran zai fitar da dubban ƙananan ’yan kasuwa daga tsarin bayan haraji a Kasar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an soke harajin COVID-19 Health Recovery Levy, yayin da harajin NHIL da GETFund za su ba da damar cire harajin shigar da kaya (input tax credit), domin ƙara gaskiya da sauƙaƙa bin doka.
Haka kuma, an dakatar da VAT Flat Rate Scheme (VFRS), inda aka maye gurbinsa da sabon tsari guda ɗaya da gwamnati ke cewa zai sauƙaƙa aiwatarwa ga dukkan ’yan kasuwa.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
