News
Albarkatun Nijeriya Ne Ke Jawo Matsin Lambar Amurka — Mahdi Shehu
Masani kan harkokin siyasa, Mahdi Shehu, ya ce matsin lambar da Amurka ke yi wa Nijeriya ba ta da alaƙa da addini ko manufofin dimokiraɗiyya, sai dai tana da nasaba kai tsaye da albarkatun ƙasa da Allah Ya albarkaci ƙasar da su.
Shehu ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan dangantakar Nijeriya da Amurka, inda ya zargi Washington da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu ƙasashe, musamman masu yalwar albarkatu.
A cewarsa, Amurka na ɗaukar kanta a matsayin ‘yansandan duniya’, alhali tana fuskantar manyan ƙalubale na tsaro da tattalin arziƙi a cikin ƙasarta.
Masani kan siyasar ya ce Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke da dimbin ma’adinai masu daraja, lamarin da ke ƙara jan hankalin manyan ƙasashen duniya tare da haifar da matsin lamba ta hanyoyi daban-daban.
Ya kuma zargi ƙasashen Yamma da hana Nijeriya damar samun fasaha da horon da take buƙata domin tinkarar matsalolin rashin tsaro da ke addabar ƙasar.
Shehu ya ce irin waɗannan ƙuntatawa na sa ƙasashe masu tasowa su dogara da waje, maimakon gina ƙarfinsu na cikin gida.
A ra’ayinsa, ya dace Nijeriya ta faɗaɗa alaƙarta da ƙasashe irin su China da Rasha, inda ya ce muradunsu sun fi karkata ga ayyukan ci gaba idan aka kwatanta da na Amurka da sauran ƙasashen Yamma.
Ya ce ayyukan gine-ginen da China ke tallafawa a Afirka sun fi kasancewa a bayyane tare da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma, yayin da rancen kuɗi daga ƙasashen Yamma ke jefa ƙasashe cikin matsin tattalin arziƙi da dogon bashi.
Mahdi Shehu ya jaddada cewa sauye-sauyen tsarin duniya na tafiya ne a hankali, kuma ƙasashen da suka fahimci muradunsu tare da zaɓar abokan hulɗa masu amfani za su fi samun damar kare ‘yancinsu da ci gabansu a nan gaba.
