News
KALVEJ Ƙungiya Ce Mai Zaman Kanta Ta, Ba Ta Ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai — Waiya
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa Ƙungiyar ’Tsofaffi yan Jaridu ta Kano (KALVEJ) ƙungiya ce ta ƙwararru Mai Zaman Kanta su, wadda ba reshe ba ce ta Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta jihar.
Waiya ya faɗi hakan ne yayin zaman tantancewa da amincewa da Tsarin shugabancin Ƙungiya KALVEJ, inda ya ce duk wata hulɗa tsakanin ma’aikatar da ƙungiyar tana gudana ne bisa ƙa’idojin aikin jarida ba tare da katsalandan a harkokin cikin gida na ƙungiyar ba.
Albarkatun Nijeriya Ne Ke Jawo Matsin Lambar Amurka — Mahdi Shehu
A cewarsa, kiyaye ’yancin ƙungiyoyin ƙwararru na taimaka musu su yi aiki yadda ya kamata, tare da bin ka’idojin da ake bi a duniya.
Ya ƙara da cewa ma’aikatar na da irin wannan dangantaka ta ƙwararru da ƙungiyoyi irin su NUJ da NIPR, da sauran ƙungiyoyin da ke da alaƙa da aikin sadarwa.
An amince da Tsarin shugabancin ne a Tahir Guest Palace da ke Kano, a wani zama da ya haɗa mambobin ƙungiyar daga fannoni daban-daban na aikin jarida, ciki har da malamai na jami’o’i.
Daga cikin batutuwan da mambobi suka jaddada akwai rashin fayyace tanade-tanaden walwalar mambobi, wakilcin jinsi, da kuma hanyoyin samun kuɗaɗen shiga masu ɗorewa domin tafiyar da harkokin ƙungiyar.
A ƙarshen zaman, mambobi sun amince da ƙudurin bai wa kwamitin damar ci gaba da tafiyar da harkokin ƙungiyar na shekara guda, kafin a gudanar da zaɓen shugabanni na dindindin.
Shugaban kwamitin, Alhaji Ahmed Aminu, ya gode wa mambobi bisa amincewar da suka nuna, tare da tabbatar da cewa za a yi la’akari da dukkan matsalolin da aka taso da su, musamman waɗanda suka shafi walwalar mambobi.
