Connect with us

News

‎FAAN Na Shirin Ƙara Harajin Jigilar Kaya

Published

on

FAAN

Ana fargabar tangarda a ayyukan filayen jiragen sama a faɗin Najeriya daga ranar Litinin, yayin da wakilan masu safarar kaya ke barazanar gudanar da zanga-zanga kan shirin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) na ƙara kuɗin harajin jigilar kaya.

‎Rahotanni sun nuna cewa FAAN na shirin fara aiwatar da sabon tsarin haraji daga ranar 2 ga Fabrairu, 2026, inda za a ƙara kuɗin daga naira 7 zuwa naira 25 kan kowanne kilo. Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, inda ake gudanar da mafi yawan jigilar kaya ta sama a Najeriya.

Advertisement

‎FAAN Na Shirin Ƙara Harajin Jigilar Kaya

‎Wasu jami’an FAAN sun tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin fara aiwatar da sabon tsarin, duk da adawar da masu safarar kaya da sauran masu ruwa da tsaki ke nunawa.

‎Masu safarar kayan sun ce ƙarin harajin zai ƙara musu nauyi tare da barazana ga kasuwancinsu, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsadar kaya da kuma rage yawan jigilar kaya ta sama a ƙasar.

Advertisement

‎Sai dai FAAN ta kare matakin da cewa ƙarin harajin ya biyo bayan gyare-gyaren cikin gida da aka aiwatar domin inganta ayyuka da kuma tsarin tattara kuɗaɗen shiga.

‎Wani babban jami’in hukumar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an ɗage fara aiwatar da sabon tsarin tun farko domin daidaita ayyuka da kuma rufe hanyoyin asarar kuɗaɗen shiga.

Advertisement

‎“Yanzu an kammala gyare-gyaren, kuma muna da tabbacin cewa sabon tsarin zai inganta kuɗaɗen shiga,” in ji jami’in.

‎A gefe guda kuma, Ƙungiyar Africa Association of Professional Freight Forwarders and Logistics of Nigeria ta ce matakin bai zo a kan kari ba, tana mai gargaɗin cewa zai dagula harkar jigilar kaya tare da ƙara tsadar kasuwanci.

Advertisement

‎Shugaban ƙungiyar, Frank Ogunojemite, ya ce ƙarin daga naira 7 zuwa naira 25 kan kilo zai iya rage fitar da kaya waje, ƙara tsadar shigo da kaya, tare da jefa ƙarin nauyi kan ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki a Najeriya.

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending