News
NELFUND Ta Tsawaita Wa’adin Cike Neman Lamunin Karatu Ga Dalibai
Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Ƙasa (NELFUND) ya tsawaita wa’adin cike neman lamunin na zangon karatun shekarar 2025/2026 daga ƙarshen watan nan na Janairu har zuwa 27 ga watan Fabrairu mai kamawa.
Sanarwar ta fito ne ta bakin Daraktan Sadarwa na Dabaru na asusun, Oseyemi Oluwatuyi, a wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis.
FAAN Na Shirin Ƙara Harajin Jigilar Kaya
A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa masu neman lamunin ƙarin lokaci su kammala cike fom ɗin neman lamuni, tare da tabbatar da cewa babu wani ɗalibi da ya cancanta da za a bari a baya saboda ƙarancin lokaci.
Shugaban gudanarwa na NELFUND, Akintunde Sawyerr, ya ce tsawaita wa’adin na nuna ƙudirin asusun wajen tabbatar da adalci da bai wa kowane ɗalibin Najeriya damar cin gajiyar shirin.
“Wasu daga cikin masu nema na buƙatar ƙarin lokaci domin kammala bayar bayanansu.
Wannan mataki zai tabbatar da cewa kowane ɗalibi da ya cancanta ya samu dama ɗaya ta amfana da asusun,” in ji Sawyerr.
Ya kuma yi kira ga duk ɗaliban da ba su kammala cike fom ɗin neman lamunin ba da su yi amfani da wannan damar, tare da tabbatar da cewa sun tura dukkan bayanan da ake buƙata kafin 27 ga Fabrairu.
NELFUND ta ce za ta ci gaba da bayar da ƙarin bayanai da sabbin sanarwa ta kafafen sadarwarta na hukuma, ciki har da imel info@nelf.gov.ng, da shafukan sada zumunta da kuma shafin yanar gizon ta na hukuma.
