Connect with us

News

An Kama Wasu Ma’aurata Bisa Zargin Yi Garkuwa Da Kansu, Tare Da Karɓar Naira Miliyan 10 Matsayin Kudin Fansa

Published

on

Garkuwa

An kama wasu ma’aurata mazauna jihar Legas bisa zargin su da kitsa garkuwa da kansu tare da karɓar Naira miliyan 10 daga dangi da abokansu a matsayin kudin fansa.

Aminiya ta gano cewa ma’auratan, masu suna Fred da Goodness, sun ƙirƙiri labarin sacewar a ranar 7 ga watan Janairu domin neman kuɗi ga mijin, wanda ya yi niyyar komawa Amurka saboda rashin tallafin kuɗi.

Advertisement

‎NELFUND Ta Tsawaita Wa’adin Cike Neman Lamunin Karatu Ga Dalibai ‎

Wani jami’in ’yan sanda da ya yi magana da Jaridar a ranar Alhamis ya ce ma’auratan sun tuntubi ’yan uwa daga danginsu, suna ikirarin cewa an sace su tare da neman kudin fansa.

Advertisement

Dangin sun tattara Naira miliyan 10 cikin kwana uku, suna zaton kuɗin zai taimaka wajen kubutar da su.

Jami’in ya ce ma’auratan sun tsara wurin karɓar kuɗin a wata makaranta da ke Cappa, Mushin.

Advertisement

“Jami’an da ke sa ido sun lura da matar ta shiga wurin ita kaɗai, daga baya mijin ya iso. Amma an fara zargin su bayan sun fito tare da jakar kuɗi. An bincika jakar, aka gano kudin fansa, nan take aka kama su,” in ji shi.

Matar ta bayyana cewa ita ce ta shawarci mijinta su kitsa wannan shiri.

Advertisement

Tuni dai aka mika su ga ’yan sanda, inda bincike ya tabbatar da cewa su suka kitsa garkuwar da kansu.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Abimbola Addebisi, ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Advertisement

Ko a watan Disamba 2025, Aminiya ta ruwaito yadda aka kama wata mata mai shekaru 26 da aka bayyana da sunan Misturah, bisa zargin kitsa sace kanta tare da karɓar Naira miliyan 2.5 daga mijinta a matsayin kudin fansa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending