Connect with us

News

DSS Sun Kubutar Da Sakataren Karamar Hukumar Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Kano 

Published

on

Dss
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta sanar da kubutar da Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Kibiya da ke Jihar Kano, Hon. Hamza Musa Durba, bayan da aka yi garkuwa da shi.

A cewar rahotanni, jami’an tsaron sun gudanar da wani samame a wani daji da ke yankin Kibiya, inda suka samu nasarar ceto jami’in gwamnati ba tare da ya samu wata illa ba.

Ƴan Kasuwa Sun Ƙi Sauko Da Farashin Mai Duk Da Raguwar Sa A Kasuwar Duniya

Advertisement

Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an sun fara tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da shi ta wayar tarho, lamarin da ya taimaka musu wajen gano maboyar wadanda ake zargin.

Rahoton ya kara da cewa jami’an DSS sun kama mutane biyu daga cikin wadanda ake zargi, inda aka same su da bindiga kirar AK-47.

A halin yanzu, hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a lamarin.

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending