Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya Za Ta Ɓullo Da Lambar Tantance Ɗalibai Tun Daga Matakin Firamare

Published

on

FB IMG 1762488671790 768x511

Gwamnatin Tarraya ta sanar da ɓullo da wata lambar tantance ɗalibai ta baiɗaya domin bibiyar karatunsu tun daga matakin firamare.

Ministan ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da manema labarai a jihar Legas a ranar Asabar kamar yadda jaridar Tribune ta rawaito.

Advertisement

Gwamnan Kano Ya Umurci Jami’an Gwamnatinsa Da Ke Son Yin Takara Da Su Yi Murabus

Haka kuma, mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta musanta rahotannin da ke cewa gwamnatin za ta soke jarrabawar shiga ƙaramar sakandare da ɗalibai ke rubutawa bayan kammala firamare.

Advertisement

 

Game da lambar tantance ɗalibai:

Advertisement

 

Alausa ya yi bayanin cewa, lambar tantance ɗaliban za ta taimaka wajen bibiyar ɗalibai ko da kuwa sun canja makarantar da suke zuwa.

Advertisement

 

Ya kuma ce sabon tsarin zai magance giɓin da ake da shi na ci gaba da karantu da ake samu daga firamare zuwa sakandare musamman game da yawan yaran da ba sa samun damar ci gaba da makaranta.

Advertisement

 

“Idan yaro ya kamata a ce yana JSS 1, amma bai shiga ba, za mu iya sanin me ya sa bai ci gaba da karantu ba,” in ji Alausa.

Advertisement

 

A cewarsa a cikin ɗalibai miliyan 23 daga makarantun gwamnati sama da miliyan 50,000 a ƙasar nan, bai fi yara miliyan 3 ne ke ci gaba da karatu zuwa ƙaramar sakandare.

Advertisement

 

“Tambayar ita ce, ina sauran ɗalibai sama da miliyan 20 da ba a sa su a makarantar sakandare ba?” ya shiga tunani.

Advertisement

Mista Alausa ya ce, babbar matsalar ita ce rashin samun dama.

Ya ƙara da cewa ya gana da ƙungiyar gwamnonin Najeriya kan akwai buƙatar gina ƙarin makarantu da za su bai wa yara da dama damar zuwa makaranta.

Advertisement

“Domin bibiyar ɗalibai yara da manya, za mu ɓullo da lambar tantancewa tun daga firamare. Za ta zama lamba keɓantacciya ga yara kuma za ta zama lambarsu a kowacce makaranta suke ko aka mayar da su,” ya yi ƙarin haske.

Ministan ya ce, akwai yunƙuri na dawo da ciyarwa a makarantu domin ƙarfafa guiwa wajen sa yara a makarantu, yana mai cewa shirin za a mayar da shi ne ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi ta ƙasa don inganta yadda ake sa ido a kan shirin.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending