Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Cafke Sojan Bogi Da Wasu Biyar Kan Rikicin Jos

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da karyar soja ne, tare da wasu mutum biyar da ake dangantawa da tashin hankalin da ya faru a wasu sassan birnin Jos.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Alfred Alabo, ya shaida wa manema labarai cewa an cafke mutumin ne a unguwar Angwan Rukuba, wuri guda da aka kai hari a daren Lahadin Palm Sunday, inda mutane 28 suka mutu yayin da wasu 22 suka jikkata.

Advertisement

Ya ce an kama wanda ake zargin ne da yammacin ranar Laraba, yayin da yake yawo cikin yanayi mai tayar da hankali, sanye da tufafin da suka yi kama da na soja.

“Mun same shi da katin shaida na bogi na makarantar soji ta Najeriya (NMS),” in ji Alabo.

Advertisement

Kazalika, rundunar ‘yan sandan ta ce ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a rikice-rikicen da suka faru a cikin garin Jos, inda ta bayyana su a matsayin ‘yan daba da suka yi anfani da halin da ake ciki wajen aikata sata.

“Sun rika kwace kudade da kayayyaki daga hannun jama’a, musamman a yankin Terminus,” in ji shi.

Advertisement

Ya kara da cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar daukar mataki domin dakile lamarin, inda suka tarwatsa ‘yan daban tare da dawo da zaman lafiya.

Rundunar ta kuma ce an kara tsaurara matakan tsaro a wurare masu muhimmanci a fadin birnin, domin kare rayuka da dukiyoyi.

Advertisement

‘Yan sanda sun bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da sanya ido, tare da sanar da jami’an tsaro duk wani abu da ya dauki hankali.

 

Advertisement

CHANNELS TV

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending