Connect with us

News

ADC Ta Zargi INEC Da Yi Wa Gwamnatin Tinubu Aiki Don Lalata Jam’iyyun Hamayya

Published

on

ADC

Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da yin aiki ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin lalata jam’iyyun adawa a Najeriya.

A sanarwar da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce jam’iyyar ta yi watsi da fassarar da INEC ta yi kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, tana mai cewa matakin ya nuna alamun matsin lamba daga gwamnati.

Advertisement

Babban Bankin CBN Ya Fitar Da Sunayen Bankuna 33 Da Suka Cika Ƙa’idar Ƙara Jarinsu

Jam’iyyar ta bayyana cewa bayanin da INEC ta fitar na cike da sabani da kuma rashin daidaito da gaskiyar abin da kotu ta yanke, inda ta zargi hukumar da karkata ga bangaren gwamnati.

Advertisement

ADC ta ƙara da cewa tana nazarin matakan da za ta ɗauka nan gaba, tare da kira ga mambobinta da sauran ‘yan Najeriya da su ci gaba da tsayawa tsayin daka yayin da ake jiran mataki na gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending