News
Gidauniyar Dr. Aminu Magashi Garba Tana Ci Gaba Da Tallafa Wa Gajiyayu A Kano
Gidauniyar Dr. Aminu Magashi Garba ta ce za ta ci gaba da bayar da tallafin magunguna da kayan abinci ga asibitocin gwamnati a Jihar Kano, a wani yunkuri na rage radadin talauci da taimakawa marasa ƙarfi.
A wannan karo, gidauniyar ta kai ziyara Gidan Gajiyayu da ke Shahuchi, inda ta raba kayan abinci da magunguna kyauta ga mazauna cibiyar.
An yi musayar bayanai tsakanin wakilan Amurka da Iran a Islamabad
Da yake jawabi a wurin, shugaban gidauniyar, Dr. Aminu Magashi Garba, ya bayyana cewa sun haɗa gwiwa da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu domin tallafawa marasa lafiya da gajiyayu.
Ya ce wannan haɗin gwiwa na da nufin rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta sakamakon talauci, musamman ga waɗanda ba su da ƙarfi.
A nasa jawabin, shugaban SEMA ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa idan sauran masu ruwa da tsaki da ‘yan siyasa a Kano za su yi koyi da irin wannan aiki, za a samu sauƙi a matsalolin da al’umma ke fuskanta.
Rahotanni daga wakiliyarmu Safiya Muhammad Usman sun nuna cewa Dr. Magashi ya ce suna shirin kai irin wannan tallafi zuwa wasu ƙananan hukumomi, ciki har da Danbatta da Munjibir da Karaye da Tudun Wada da kuma Sumaila.
Haka kuma ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su ƙara ba da gudummawa wajen tallafawa masu fama da larurar kwakwalwa da sauran gajiyayu, domin rage radadin rayuwa a tsakanin al’umma.
