News
An Samu Yaɗuwar Makamai Sama Da Miliyan Biyar A Najeriya — Bincike
Wani bincike mai zurfi ya bankado cewa yaduwar haramtattun makamai a Najeriya ta kai sama da miliyan biyar, abin da ke ƙara tsananta matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.
Binciken, wanda wata cibiyar kula da makamai a Najeriya ta gudanar, ya nuna cewa yankin Kudu maso Yamma na daga cikin wuraren da ke fuskantar barazanar yawaitar wadannan makamai.
Dr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
Da yake jawabi ga manema labarai, daraktan cibiyar a shiyyar, CP Abiodun Alamutu (mai ritaya), ya danganta wannan matsala da raunin tsaron iyakokin ƙasar, yana mai cewa hakan ne ke bai wa masu safarar makamai damar shigo da su cikin sauƙi daga ƙasashen waje.
Ya ce, duk da wasu ƙididdiga na baya da ke nuna cewa makaman sun kai miliyan biyar, sabbin bayanan da cibiyar ta tattara sun tabbatar da cewa adadin na iya wuce haka.
A wani ci gaba, Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana cewa ta kama manyan kwantenoni guda tara dauke da makamai, alburusai, muggan ƙwayoyi da kuma kayayyakin gwanjo da aka shigo da su daga ƙasar Turkiyya.
Masana harkokin tsaro sun jaddada cewa yawaitar wadannan makamai na taka muhimmiyar rawa wajen rura wutar ayyukan ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Cibiyar ta kuma bayyana cewa tana ƙara mayar da hankali kan dabarun kwace makamai daga hannun jama’a, ta hanyar haɗin gwiwa da sarakuna, shugabannin al’umma da ƙungiyoyi masu zaman kansu, domin ƙarfafa mutane su mika makaman da ke hannunsu cikin lumana.
Wannan bincike na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙara zage damtse wajen rage yaduwar makamai, inda a baya-bayan nan aka lalata sama da makamai 2,800 a Abuja, a wani yunƙuri na daƙile barazanar tsaro a ƙasar nan..
