News
Jami’an NDLEA Sun Kama Tsofaffi Masu Shekaru 83 Da 78 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA), ta sake cafke wasu dattawa biyu masu shekaru 83 da 78 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Lamarin ya kara jawo hankali ganin yadda ake samun karuwar tsofaffi da ke shiga harkar fataucin kwayoyi a kasar.
Dakarun Sojin Sama Sun Lalata Maboyar ‘Yan Bindiga A Katsina
Rahotanni sun nuna cewa wannan kama na zuwa ne bayan wani bincike da jaridar Leadership Newspaper ta fitar a makon da ya gabata, wanda ya bayyana wani sabon salo na yadda wasu tsofaffi ke shiga harkar miyagun kwayoyi. Hukumar NDLEA ta ce ta samu nasarar cafke mutanen ne bayan tattara bayanan sirri da kuma gudanar da sahihan bincike.
Masana sun bayyana cewa matsin tattalin arziki da kuma yaudarar masu fatauci na daga cikin dalilan da ke jefa wasu tsofaffi cikin wannan hadari. NDLEA ta jaddada kudurinta na ci gaba da yaki da fataucin miyagun kwayoyi tare da gargadin cewa ba za ta sassauta wa kowa ba, ko da kuwa shekaru sun ja.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
