Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Satar Ragunan Layya 18 

Published

on

Ram 768x530

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekara 58 bisa zargin satar raguna 18 a cikin garin Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Bauchi.

Advertisement

Shugaba Tinubu Bai Da Shirin Sauya Sunan Najeriya Da Soke Shari’a A Arewa  —Fadar shugaban kasa

A cewarsa, jami’an rundunar sun samu bayanan sirri inda suka tare wata farar motar bas kirar Hummer da kuma wata mota kirar Toyota Camry mai launin toka a kan titin Gubi a ranar 19 ga watan Mayu.

Advertisement

Ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ake ɗauke da raguna 18 da ake kyautata zaton an sato su.

SP Habib ya bayyana cewa mutumin ɗan garin Tahoua ne da ke jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Advertisement

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya haɗa kai da wasu mutum biyar da har yanzu suke tsere wajen satar ragunan daga wani wuri da ke kusa da gidan mai na A.A. Kunya da ke kan titin Murtala Mohammed Way a Bauchi.

Kakakin rundunar ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da mutumin da aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike.

Advertisement

 

 

Advertisement

PLATINUM POST NEWS 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending