Connect with us

News

Ƴansanda Sun Kama Shugaban Hukumar PFIPC Ta Boge Adeniyi Bayan Umarnin Kotu

Published

on

1784076705048

Rundunar ƴan sandan Najeriya sun kama Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin cewa shi ne babban darakta hukumar PFIPC, sa’o’i kaɗan bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da sammacin kama shi.

Mai magana da yawun ƴan sandan a jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an daga Abuja ne su ka kama Adeyemi a maɓoyarsa da ke jihar Osun, kuma a na sa ran za a mayar da shi Abuja domin ci gaba da shari’a.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Mai Garkuwa Da Mutane Ne A Kano

Wani faifan bidiyo da ya bayyana ya nuna Adeyemi sanye da kayan gargajiya masu launin shuɗi yayin da jami’an tsaro su ka kewaye shi. A lokacin da a ka tambaye shi ya bayyana sunansa, ya ƙi amsa kai tsaye, ya na mai cewa ya riga ya faɗi sunansa sau da dama.

Ana zargin Adeyemi da haɗa baki, ƙirƙirar takardun bogi da kuma yin sojan gona ta hanyar gabatar da kansa a matsayin babban na wata hukuma da fadar shugaban ƙasa ta ce babu ita.

Kotun ta yi watsi da hujjar lauyansa cewa bai halarci zaman ba saboda tsoron rasa ransa, tare da jaddada cewa dole ne ya gurfana domin fuskantar shari’a.

Advertisement

Daga nan kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Satumba, 2026, domin fara gurfanar da shi.

Haka kuma ya sake jaddada zarginsa cewa ya biya Naira miliyan 400 ta hannun wani mutum domin samun muƙamin na wannan hukuma mai cece-kuce, tare da kira da a gudanar da bincike.

Idan aka same shi da laifin ƙirƙirar takardun bogi, zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru har 21 ba tare da zabin biyan tara ba, yayin da laifin yin sojan gona ke ɗauke da hukuncin daurin shekaru har uku ko kuma biyan tara.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending