Connect with us

Labarai

Shekaru 50 Da Kafuwa: Tsofaffin Ɗaliban GSS Dawakin Kudu Sun Ƙaddamar Da Littafin Tarihi Da Asusun Tallafi

Published

on

IMG 20261116 WA00631 768x508
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Tsofaffin ɗaliban makarantar Government Secondary School, Dawakin Kudu (GSSDK), sun ƙaddamar da littafin tarihin makarantar da kuma asusun tallafa wa ɗalibai marasa ƙarfi da mambobin ƙungiyar, yayin bikin cika shekaru 50 da kafuwarta.

An gudanar da bikin murnar cika shekaru 50 na makarantar a ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026, a Kwalejin Kimiyya ta Sani Bello da ke Dawakin Kudu, Jihar Kano.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Takwas Bayan Rikicin Siyasar Da Ya Barke A Bichi

Taron ya samu halartar tsofaffin ɗaliban makarantar, manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Babban abin da ya fi daukar hankali a wajen taron shi ne ƙaddamar da wani littafi mai suna Almost Forgotten: The Legacy of GSS Dawakin Kudu and Its Pioneer Students (1975–1977), wanda Injiniya Yasin Garba Maisikeli, ɗaya daga cikin ɗaliban farko na makarantar, ya rubuta.

 

Advertisement

Haka kuma, ƙungiyar ta ƙaddamar da asusun tallafa wa ilimi da jin daɗin mambobinta, wanda aka tsara domin taimaka wa ɗalibai masu hazaƙa amma marasa hali, mambobin da ke fuskantar matsaloli da kuma iyalan waɗanda suka rasu.

 

Da yake gabatar da littafin, marubucin, Injiniya Yasin Garba Maisikeli, ya ce littafin zai taimaka wajen adana tarihin makarantar da gudunmawar ɗaliban farko domin amfanin al’ummomin da ke yanzu da waɗanda za su zo nan gaba.

 

Ya bayyana cewa ɗaliban farko sun fara karatu a makarantar a shekarar 1975, inda suka fito daga wurare daban-daban, kuma makarantar ta taka muhimmiyar rawa wajen gina tarbiyyarsu da shirya su domin fuskantar ƙalubalen rayuwa.

 

Advertisement

A cewarsa, makarantar ba ta tsaya ga koyar da darussa kawai ba, domin ta koyar da ɗalibai ladabi, jajircewa, ɗaukar nauyi da kishin al’umma.

 

Ya ce littafin mai shafuka sama da 500 ya ƙunshi hotuna, takardu, tarihin rayuwa da bayanai daban-daban da suka shafi kafuwar makarantar da ci gabanta.

 

Maisikeli ya bayyana cewa rubuta littafin ya zama wajibi domin kauce wa mantawa da muhimman abubuwan da suka faru a makarantar, musamman ganin yadda shekaru ke ƙaruwa kuma tsofaffin ɗaliban ke watsewa.

 

Advertisement

Ya kuma bayyana fatan cewa makarantar za ta iya bunƙasa zuwa babbar cibiyar ilimi, kamar kwalejin kimiyya da fasaha ko jami’ar kimiyya da fasaha ta Sani Bello.

 

A nasa jawabin, tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya jagoranci taron, ya jaddada muhimmancin ilimi wajen ci gaban mutum da al’umma.

 

Shekarau ya yaba wa tsofaffin ɗaliban bisa ƙoƙarin tattara tarihin makarantar, yana mai cewa rubuta tarihin irin waɗannan cibiyoyi na taimakawa wajen adana nasarori da darussan da al’ummomi masu zuwa za su koya.

 

Advertisement

Shi ma tsohon gwamnan mulkin soja na tsohuwar Jihar Kano, Kanal Sani Bello (mai ritaya), wanda gwamnatinsa ta kafa makarantar a shekarar 1975, ya bukaci makarantu da su mayar da hankali kan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire.

 

Sani Bello, wanda Daraktan Gudanarwa na Mainstream Energies, Lauya Siraj Abdullahi, ya wakilta, ya ce ya kamata makarantu su samar wa ɗalibai ilimin da zai ba su damar ƙirƙirar ayyukan yi da samar da hanyoyin magance matsalolin al’umma.

 

Ya jaddada buƙatar koyar da ɗalibai tunani mai zurfi, binciken kimiyya da ƙwarewar sana’o’i domin su dace da buƙatun zamani.

 

Advertisement

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana farin cikinsa da sake haɗuwa da ɗaliban farko da ya ziyarta shekaru 50 da suka gabata, waɗanda a lokacin suke tsakanin shekaru 14 zuwa 18, amma yanzu sun zama ƙwararru a fannoni daban-daban na rayuwa.

 

A nasa jawabin, masanin ilimi da kafafen yaɗa labarai na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya bukaci ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai a Najeriya da su wuce shirya tarukan haɗuwa kawai, su mayar da hankali wajen tallafa wa matasa da adana tarihin makarantunsu.

 

Da yake jawabi kan taken Triple Heritage: Memory, Legacy, and the Pursuit of Scholastic Excellence, Farfesa Adamu ya bayyana muhimmancin tattara tarihin makarantu kafin mutanen da suka kafa su da kuma waɗanda suka yi karatu a cikinsu su rasu.

 

Advertisement

Ya kuma bukaci tsofaffin ɗaliban da suka ƙware a fannonin injiniya, shari’a, kasuwanci da ilimi da su kafa shirye-shiryen jagoranci da horas da matasa domin taimaka musu wajen samun ƙwarewa da cimma burinsu.

 

Ya ce ya kamata ƙungiyar ta kuma samar da kundin adana takardu da hotunan makarantar ta hanyar fasahar zamani domin sauƙaƙa bincike ga masu sha’awar tarihin makarantar.

 

A nasa ɓangaren, Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Farfesa Dahiru Sale Mohammed, ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da ba ilimi muhimmanci, musamman ilimin kimiyya da fasaha.

 

Advertisement

Ya yaba wa tsofaffin ɗaliban bisa ƙoƙarin rubuta tarihin makarantar, yana mai cewa kundin zai taimaka wa masu bincike da ɗalibai wajen fahimtar tarihin makarantar da sauye-sauyen da ta samu tun kafuwarta.

 

Da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban, Abubakar Musa Omar, ya bayyana bikin a matsayin wata dama ta ƙarfafa zumunci tsakanin mambobi da kuma samar da hanyoyin tallafa wa ci gaban makarantar.

 

Ya ce ƙaddamar da asusun tallafin zai samar da tsayayyen tsari na taimaka wa ɗalibai masu ƙwazo amma marasa hali, mambobin da ke cikin matsanancin hali da iyalan waɗanda suka rasu.

 

Advertisement

Abubakar ya bayyana cewa gudunmawar kuɗi da ta fuskar shawarwari da Kanal Sani Bello (mai ritaya) ya bayar ce ta taimaka wajen ganin an wallafa littafin tarihin makarantar.

 

Ya kuma bayyana burin ƙungiyar na ganin Sani Bello Science College ta bunƙasa zuwa babbar cibiyar ilimi, musamman a fannin kimiyya da fasaha.

 

Bikin ya samu halartar Kanal Sani Bello (mai ritaya), wanda shi ne babban baƙon gayyata kuma Lauya Siraj Abdullahi ya wakilta; Farfesa Yusuf Isa Chamo, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Jigawa, wanda ya wakilci gwamnan jihar; da Alhaji Abba Yusuf, Danmakwayon Kano kuma Hakimin Dawakin Kudu, wanda ya kasance uban bikin.

 

Advertisement

Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Sani Ahmed Mairago, ya kasance mai masaukin baki, tare da wasu tsofaffin da masu riƙe da muƙaman majalisun dokoki, masana ilimi da sauran manyan baki.

 

Ƙungiyar ta gode wa dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen gudanar da bikin da kuma ƙaddamar da ayyukan da za su taimaka wajen inganta ilimi da walwalar mambobinta.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending