News
Gwamnan Kogi ya dakatar da Sarkin Eganyi saboda matsalar tsaro
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Gwamnatin jihar Kogi da ke arewa maso tsakiyar kasar ta dakatar da mai martaba Sarkin Eganyi, Alhaji Musa Isa Achuja daga mukaminsa, sakamakon tabarbarewar tsaro a yankinsa.
Gwamna Alhaji Yahaya Bello ne ya ba da umurnin dakatar da mai martaba sarkin, wanda aka fi sani da Ohi, daga mukamin nasa, bisa zarginsa da sako-sako da al’amuran da suka shafi tsaro a yankin karamar hukumar Ajaokuta.
Gwamnan ya dauki matakin dakatar da sarkin ne bayan wani bincike da jami`an tsaro suka yi, wanda aka karshe suka cafke sarkin.
Yan Kannywood na mayar da martani kan hana su amfani da kayan ‘yan-sanda
Kazalika gwamnan ya ba da umurnin a rubuta wasikar tuhuma ga shugaban karamar hukumar Ajaokuta, Honorabul Mustapha Aka`aba domin ya wanke kansa dangane da yadda tsaro ya tabarbare a yankin.
A ranar Asabar din ta da wuce ne wasu `yan bindiga suka yi wa wasu `yan sanda uku, ciki har da DPO da kuma wasu `yan sa-kai su biyar kwanton-bauna a yankin karamar hukumar Ajakutan, harin da ya yi sanadin mutuwarsu su takwas baki daya.
A cikin wata sanarwa, wadda mai magana da yawun gwamnan, Mohammed Onogwu ya sanya wa hannu, gwamna Yahaya Bello ya gargadi sarakunan jihar baki daya da su guji hada-baki ko taimaka wa miyagu ta kowace hanya wajen yin aika-aika a jihar, yana cewa gwamnatinsa za ta sa kafar-wando guda da duk mutumin da ke goya wa `yan ta`adda baya, komai girmansa.
Har wa yau, gwamnan ya haramta wa shugabannin kananan hukumi yin bulaguro zuwa wajen yankunansu ba tare da wani kwakkwaran dalili ba kuma ko da akwai dalili sai sun samu amincewar yin bulaguron.
A karshen makon da ya wuce al`umomin Jidda-Bassa da karamar hukumar Ajaokuta suka kai kuka wurin DPO, cewa wasu `yan bindiga suna far musu cikin gonakai, suka kwashe musu amfanin gona.
Daga nan ne shugaban `yan sandan ya hada mutanensa da wasu `yan sa-kai suka bazama domin ceto al`umma, amma sai suka yi rashin sa`a suka fada tarkon `yan bindigan, wadanda suka yi musu kwanton-bauna, suka halaka su.
