Connect with us

Business

Tattalin arzikin Saudiyya zai iya fin na ko ina haɓaka a duniya a bana

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Advertisements
Advertisements

Asusun lamuni na Duniya ya ce da yiwuwar tattalin arzikin Saudiyya zai iya zama mafi habbaka a duniya a wannan shekarar yayin da tattalin azrikin duniyar ke fuskantar koma baya.

A cewarsa masarautar na duba yadda za ta cimma kashi 7.6, wanda bukatar mai da ake da ita a duniya za ta matukar taimakawa da kuma habbakar bangarorin da ba na mai ba.

Karin bukatar da ake da ita ta makamashi – saboda rikicin Ukraine – ya taimaka wa manyan kasashen duniya da ke da mai wajen farfadowa daga illar da Covid-19 ta yi musu.

Har yanzu hauhawar kayan farashi a kasar bai fi kashi uku ba kacal cikin 100.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending