News
Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Sansanin Gogarman Yan Bindiga Bello Turji
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yan bindiga masu tarin yawa na sansanin fitaccen ‘dan ta’adda Bello Turji, sun sheka lahira
Jaridar PR Nigeria ta rawaito cewa an hallaka ‘yan ta’addan ne a wani samamen ba-zata da dakarun sojin rundunar Operation Forest Sanity suka kai dazukan Zamfara.
Erling Haaland na ci gaba da jan zarensa a gasar Premier
Harin ba-zatan an yi shi ne da jiragen yakin sojin sama bayan sun samu bayanan sirri.
Wata majiyar sirri ta sanar da jaridar PRNigeria cewa jiragen rundunar mayaƙan sama sun harba makamai masu linzami yankin Fakai, inda aka gano shi ne gidan Turji, a matsayin wani bangare na yaki da ta’addanci a yankin Shinkafi.
Majiya ta ce: “A halin yanzu, ba zamu iya bayyana yawan wadanda aka halaka ba.”
Advertisements
