News
Me Ake Ciki?: Bayan APC Ta Dage Kaddamar Da Kwamitin Yakin Neman Zabe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Har yanzu dai jam’iyyar APC mai mulki ba ta fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 ba, kwanaki bakwai bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dage haramcin yakin neman zabe.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage haramcin fara yakin neman zabe a hukumance a ranar 28 ga watan Satumba, sai dai Daily Trust ta ruwaito cewa har yanzu jam’iyyar APC ta kasa shawo kan rikicin da ke tsakaninta da kwamitin yakin neman zaben.
Gwamnatin Kwara Ta Dakatar Da Likitan Da Ake Zargi Da Hallaka Wasu Mata A Jihar
Kafin kaddamar da yakin neman zaben, sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Faleke, ya fitar da jerin sunayen mutane 422 na kwamitin.
Sai dai ci gaban ya samu tirjiya da kalubale daga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka hada da kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da gwamnonin da ‘ya’yan jam’iyyar kamar yadda suka yi ikrarin ba a tafi da su a cikin shirin.
Biyo bayan cece-kuce da rashin jituwar da akan jerin sunayen, babban daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya sanar da dage bikin rantsar da su.
Sai dai wata majiya daga jam’iyyar ta APC ta shaida wa wakilinmu a jiya cewa gwamnoni da NWC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na ci gaba da gudanar da ayyuka daban-daban, wanda hakan ya sa aka samu tsaikon yin sabon jerin sunayen da kaddamar da kwamitin.
Sai dai kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC da babban daraktan yada labarai, Festus Kayamo da Bayo Onanuga, ba su amsa kira ba, ko kuma amsa sakon SMS da aka aika a wayoyinsu domin jin ta bakinsu kan lamarin.
Lalong da sauran gwamnonin APC sun gana kan yakin neman zaben 2023
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a ranar Talata ya gana da wasu gwamnonin ‘yan kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar don tsara dabarun zaben 2023.
Taron ya gudana ne a shedikwatar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC da ke tsakiyar yankin kasuwanci a Abuja.
Majalisar Dattawa a ranar Talata ta bukaci Kamfanin Gas na Najeriya (NLNG) Limited da ya biya diyyar Naira biliyan 18.4 ga kusan iyalai 200 da aka saye gonakinsu a Bonny na Jihar Ribas kan hakkin mallakar bututun mai.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa, Hakan ya biyo bayan nazari da amincewa da rahoton kwamitin da’a, gata da kararrakin jama’a wanda ya binciki karar da al’ummomin suka
