Connect with us

News

Sojoji sun kama tabar wiwi ta N4.9m a Yobe

Published

on

Sojoji

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar sojoji ta haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa-maso-Gabas da ke Damaturu a jihar Yobe ta mika buhunan tabar wiwi guda 98 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 4.9 ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa.

Kwamandan sashin, Manjo-janar Koko Isoni ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke mika wa hukumar kayayyakin da aka kama a ranar Litinin a Damaturu.

Advertisement

Ɗan takarar majalisar wakilai, Abdulmumin Kofa ya karɓi mutane 2,000 zuwa NNPP

Kwamandan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Birgediya Janar Umar Mu’azu, ya ce dakarun bataliya ta 159 da ke Ƙaramar Hukumar Geidam ne su ka kama kayan a ranar 7 ga watan Oktoban 2022.

Advertisement

“Mai dakon kayan ya watsar da su, ciki har da motar da ke ɗauke da kayan lokacin da ya ga tawagar sintiri,” in ji shi.

A nasa jawabin, kwamandan NDLEA na jihar, Aliyu Yahaya, ya yabawa rundunar sojin bisa wannan kwazo, inda ya kara da cewa kowanne kunshi na tabar ya kai N50,000.

Advertisement

Yahaya wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamandan jihar, Ogar Peter, ya yaba da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro a jihar.

“Mun yi farin cikin samun wannan nasara. Wannan karimcin ya nuna hadin kai da ke tsakanin jami’an tsaro a jihar,”

Advertisement

in ji shi, ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya ta dukufa wajen dakile safarar miyagun kwayoyi a jihar.

 

Advertisement

 

Daily Nigerian

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending