News
Zan kawar da matsalar tsaro kafin na sauka daga mulki – Buhari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana son ganin ya kawar da duk wata matsalar tsaro da ke addabar ƙasar kafin ya sauka daga mulki.
Shugaban ya faɗi haka ne a wurin bikin bayar da lambobin girmamawa ga mashahuran mutanen da gwamnati ta karrama, wanda ya gudana a Abuja.
Najeriya ta hana amfani da maganin tarin da ‘ya kashe’ yara a Gambia
Ya ce yana son ya jaddada alwashin da ya sha a lokacin bikin tunawa da ranar samun ƴancin kai na ƙasar, cewar burinsa shi ne ya miƙa wa shugabannin da za a zaɓa, kasar, ba tare da wata matsalar tsaro ba.
A lokacin bikin karramawar shugaba Buhari ya kuma tunatar da waɗanda suka samu lambar girmamawar cewa ba an ba su ita ne domin kwalliya ba, sai domin tunatar da su nauyin da ke kansu a matsayin ƴan kasa nagari.
BBC
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
