News
Mun Warware Kararraki 586 Cikin Sama Da 604 Da Aka Samu A Kwara – Hukumar Korafe-korafe

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar dake karbar korafe-korafen jama’a a jihar Kwara ta ce ta warware kararraki sama da 586 daga cikin sama da 604 da aka samu kawo yanzu.
Kwamishinanta na jiha, Hon.Olawuyi Abidemi Joseph ne, ya bayyana hakan a Ilorin yayin zantawar sa da Daily Trust.
Kwankwaso ba zai halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar shugabannin kasa ba
Abidemi, wanda ya bayyana lamarin a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba, ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a kan wasu daga cikin shari’o’in.
Ya ce alhakin hukumar shi ne ta taimakawa wadanda ba su da karfin samun lauyoyi a jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa idan gwamnati ta yi kuskure, hukumar za ta binciki lamarin tare da yin adalci.
Ya bayyana cewa hukumar ba za ta shiga cikin wata kara da ta riga ta kai kotu ba
